Pars Today
Jagoran 'yan tawaye a Sudan ta Kudu, Riek Mashar, ya isa Juba babban birnin kasar, inda zai halarci bikin yarjejeniyar zaman lafiya da aka cimma da gwamnati a watannin baya.
Gwamnatin Sudan Ta Kudu ta sako wasu fursunoni na siyasa da wasu na yaki guda biyar a kokarin da take yi na cika alkawarin da ta dauka cikin yarjejeniyar sulhu na kasar da aka sanya wa hannu a watan da ya gabata.
Babban Kwamishiniyar kare hakin bil-adama na MDD Duniya ta ce mayakan 'yan tawayen Sudan ta kudu suna sace 'yan mata da nufin cin zarafi gami da yi musu fyade
Komitin tsaro na MDD ya tsawaita aikin dakarun tabbatar da zaman lafiya a kan iyakokin kasashen Sudan da Sudan ta Kudu.
Rahotanni daga Sudan ta Kudu sun bayyana cewar wasu fursunoni sun fada wa wasu masu gadin wani gidan yari a birnin Juba, babban birnin kasar inda suka kwance damarsu da kuma ci gaba da riko da ikon wajen tsare mutanen da ke helkwatar jami'an tsaro na kasar.
Tawagar yan tawaye Sudan ta kudu wadanda suka dade a kasar Demokradiyyar Kongo ta bar kasar zuwa gida ko kuma wata makobciyar kasa.
Kwamitin Kolin Kula da 'Yan Gudun Hijira na Majalisar Dinkin Duniya ta bada labarin cewa: Kasar Sudan ta Kudu ta rattaba hannu kan yarjejeniyar kula da yanayin 'yan gudun hijira a duniya.
Shugaba Salva Kiir na Sudan ta Kudu, ya bada umurnin sakin dukkan fursunonin siyasa da kuma na yaki da ake tsare dasu a kasarsa.
Majiyar gwamnatin kasar Sudan Ta Kudu ta sanar da cewa daga 2013 zuwa 2018 an kashe mutane 190,000 a fadin kasar saboda yakin basasa
Kasashen Sudan da Sudan ta Kudu sun tattaunawa kan batun aiki tare na tabbatar da sulhu da kuma karfafa alaka tsakanin kasashen biyu