Sudan Ta Kudu : Kiir Ya Sallami Fursunonin Siyasa
https://parstoday.ir/ha/news/africa-i33378-sudan_ta_kudu_kiir_ya_sallami_fursunonin_siyasa
Shugaba Salva Kiir na Sudan ta Kudu, ya bada umurnin sakin dukkan fursunonin siyasa da kuma na yaki da ake tsare dasu a kasarsa.
(last modified 2018-09-28T15:46:40+00:00 )
Sep 28, 2018 15:46 UTC
  • Sudan Ta Kudu : Kiir Ya Sallami Fursunonin Siyasa

Shugaba Salva Kiir na Sudan ta Kudu, ya bada umurnin sakin dukkan fursunonin siyasa da kuma na yaki da ake tsare dasu a kasarsa.

Akwai dai fursunoni da dama da ake tsare dasu a barikin soji a Juba babban birnin kasar.

Wannan matakin na daga cikn yarjejeniyar da aka cimma da jagoran 'yan tawayen kasar Riek Mashar, a watan da ya gabata.

Manufar cimma yarjejeniyar ta zaman lafiya shi ne kawo karshen yakin basasa da aka kwashe sama da shekara biyar ana yinsa a wannan jinjira kasa ta Sudan ta Kudu.

Yarjejeniyar da aka cimma ta kuma tanadi M. Mashar ya dawo cikin gwamnati a mastayinsa na daya daga cikin mataimakan shugaban kasar Salva Kiir sun guda biyar.