Pars Today
Kungiyar 'yan ta'adda ta IS ko kuma Da'esh ta dauki alhakin kai jerin hare-haren da suka yi sanadin mutuwar mutane a kalla 52 a kusancin Bagadaza babban birnin kasar.
A ziyara da ya kai kasashen Nijar da Chadi shugaba Ibrahim Bubakar Keita na Mali ya jaddada wajabcin kafa rundinar hadin gwiwa ta kasashen yankin Sahel don yaki da ta'addanci.
Kungiyar 'yan ta'adda ta (IS) ko kuma Da'esh ta dauki alhakin harin da ya yi sanadin mutuwar mutane 18 a yankin Sina na kasar Masar.
'Yan sandan kasashen Spain da Moroko sun yi awun gaba da wasu 'yan Moroko su biyar da wani dan Spain guda da ake zargi da kasantuwa cikin 'yan kungiyar ta'addancin da suke kashe mutane da kuma sare kansu.
Sojojin Iraki sun kusanto yankin Tal Afar a ci gaba da farmakin da suka kaddamar domin kwato yankunan karshe dake hannun 'yan ta'addan Da'esh.
Ministan harkokin wajen kasar Iran Dakta Muhammad Jawad Zarif ya bayyana cewar babu ruwan Musulunci da ayyukan ta'addancin da ake aikatawa da sunansa.
'Yan sanda a Spaniya na ci gaba da farautar wani mutum bayan harin da ya yi sanadin mutuwar mutane 13 da kuma raunana wasu sama da dari a birnin Barcelona.
Rundinar sojin Amurka a Afgnistan ta ce an kashe wani sajan ta a yakin da take da kungiyar 'yan ta'adda ta IS a yankin.
Harin Ta'addanci A Kasar Burkina Faso. ( sharhi)
A Burkina Faso an shiga zaman makoki na kwanaki uku tun daga jiya Litini bayan kazamin harin ta'addanci da ya yi sanadin mutuwar mutane 18 a wani gidan sayar da abinci a Ouagadugu babban birnin kasar.