Spaniya : Ana Ci gaba da Farautar Wani Maharin Barcelona
Aug 18, 2017 10:44 UTC
'Yan sanda a Spaniya na ci gaba da farautar wani mutum bayan harin da ya yi sanadin mutuwar mutane 13 da kuma raunana wasu sama da dari a birnin Barcelona.
Mutumin dai da 'yan sanda suka ce har yanzu yana yawo a binin, ana zargin cewa shi ne matukin babbar motar data banke mutane a birnin na Barcelona, kafin daga bisani ya arce.
An dai cafke wasu mutane da dama da ake zargi da hannu a harin kamar yadda hukumomin kasar suka tabbatar.
Kungiyar 'yan ta'adda ta IS ce ta dauki alhakin kai harin, a yayin da duniya ke ci gaba da aikewa da sakwanin jaje ga gwamnatin ta Spaniya.
Tags