-
Gwamnatin Maroko Tana Ci Gaba Da Murkushe Makircin Kungiyoyin 'Yan Ta'adda A Kasar
Apr 13, 2017 11:12Cibiyar leken asirin kasar Maroko ta sanar da rusa wata kungiya mai kwadaitar da matasa zuwa ga ayyukan ta'addanci musamman shiga cikin kungiyar Da'ish mai kafirta musulmi.
-
Masar : An Tantance Maharin Cocin Alexandri
Apr 13, 2017 05:54Ma'aikatar harkokin cikin gidan kasar Masar ta ce ta gano mutumin da ake zargin shine ya shirya harin kunar bakin wake wanda ya kashe kansa a cocin KIfdawa ta Saint Mark a Alexandria, harin da yayi sanadiyyar mutuwar mutane 17.
-
Sharhi : Tababa Kan Wanda Ya Kai Hari Da Makami Mai Guba A Syria
Apr 05, 2017 06:00Duniya na ci gaba da yin Allah-wadai da amfani da makami mai guba kan fararen hula a Syria, a daidai lokacin da ake ta tababa akan kowa keda hannu akan wannan aika-aikar.
-
Jami'an Tsaro: Dan Asalin Kasar Kyrgyzstan Ne Ya Kai Harin Saint Petersburg Na Kasar Rasha
Apr 04, 2017 16:48Hukumomin tsaron kasar Kyrgyzstan sun bayyana cewa wani dan asalin kasar shi ne ya kai harin kunar bakin waken da aka kai tashar jirgin karkashin kasa da ke Saint Petersburg na kasar Rasha a jiya Litinin da yayi sanadiyyar mutuwar mutane kimanin 14 da raunana wasu da dama.
-
Larijani: Pentagon Da CIA Su Ne Manyan Masu Daure Wa Ta'addanci Gindi
Apr 02, 2017 04:54Shugaban majalisar shawarar Musulunci ta kasar Iran Dakta Ali Larijani yayi kakkausar suka ga tsoma bakin da Amurka take yi cikin lamurran cikin gidan kasashen Gabas ta tsakiya yana mai cewa Amurkan tana da alaka ta kut da kut da dukkanin ta'adda da kuma ta'addancin da ke faruwa a yankin.
-
Gwamnatin Haramtaciyar Kasar Isra'ila Ita Ce Ke Karfafa Ayyukan Ta'addanci
Mar 28, 2017 05:39Ministan watsa labaran kasar Jordan ya bayyana cewa: Ci gaba da bakar siyasar gwamnatin haramtacciyar kasar Isra'ila yana daga cikin dalilan kara karfafa da watsuwan ayyukan ta'addanci a yankin gabas ta tsakiya.
-
An Hallaka Wani Jigon Al-Qaida A Afganistan
Mar 26, 2017 05:44Ma'aikatar tsaron Amurka ta sanar da hallaka wani babban jigon kungiyar 'yan ta'adda ta Al-Qaida mai suna Qari Yasin a wani harin jirgi marar matuki a Afganistan.
-
Kasar Birtaniya Ta Bukaci Hadin Kan Duniya A Fagen Yaki Da Ta'addanci
Mar 24, 2017 04:40Ministan harkokin wajen kasar Birtaniya ya bukaci duniya da ta mike tsaye a fagen yaki da duk wata barazanar ta'addanci.
-
Kungiyar Da'esh (ISIS) Ta Dauki Alhakin Harin Ta'addancin Da Aka Kai Birtaniyya
Mar 23, 2017 16:33Kungiyar ta'addancin nan ta Da'esh (ISIS) ta sanar da cewa ita ce ta kai harin ta'addancin da aka kai majalisar dokokin Birtaniya a jiya Laraba, wanda ya yi sanadin mutuwar akalla mutane biyar ciki har da wanda ya kai harin.
-
Sarkin Morocco Ya Jaddada Aniyar Gwamnatin Kasar Ta Yaki Da Masu Tsaurin Ra'ayin Addini
Mar 12, 2017 12:07Sarkin kasar Morocco ya jaddada yin kira ga kungiyoyi musamman na fararen hula kan su fadaka tare da hada kai waje guda da nufin yaki da masu tsaurin ra'ayin wuce gona da iri kan al'umma da sunan addini.