Masar : An Tantance Maharin Cocin Alexandri
Ma'aikatar harkokin cikin gidan kasar Masar ta ce ta gano mutumin da ake zargin shine ya shirya harin kunar bakin wake wanda ya kashe kansa a cocin KIfdawa ta Saint Mark a Alexandria, harin da yayi sanadiyyar mutuwar mutane 17.
A wata sanarwar da aka rabawa manema labarai, ma'aikatar harkokin cikin gidan ta ayyana Mahmoud Hassan Mubarak daga birnin Suez, da cewa shi ne ya kitsa harin.
An haifi mutumun ne a ranar 28, ga watan Satumbar 1986 a Qena na kasar ta Masar, kuma ya taba yin aiki da kamfanin manfetur na kasar.
A ranar Lahadi ne, wasu tagwayen boma bomai suka tashi a cocin dake lardin Gharbiya da lardin Alexandria a arewacin kasar ta Masar, inda mutane 45 suka mutu, sannan wasu 120 suka samu raunuka.
Harin dai na Alexandri ya yi sanadin mutuwar kiristoci 11 da kuma musulmi jami'an 'yan sandan shida a ranar Lahadin da ta gabata.