An Hallaka Wani Jigon Al-Qaida A Afganistan
Ma'aikatar tsaron Amurka ta sanar da hallaka wani babban jigon kungiyar 'yan ta'adda ta Al-Qaida mai suna Qari Yasin a wani harin jirgi marar matuki a Afganistan.
Wata sanarwa da ma'aikatar ta Pentagone ta fitar ta ce an hallaka Qari a ranar 19 ga watan nan a wani hari da Amurka ta kai a yankin Paktika dake gabashin kasar Afganistan a iyaka da Pakistan.
An dai tuhumi Qari Yasin wanda dan asalin kasar Pakistan ne a yankin kudu maso yamma na yankin Balutchistan da aikata laifukan ta'addanci da dama.
Daga cikin hare haren da Qari Yasin ya kai da akwai wanda ya yi sanadin mutuwar gomman mutane ciki har da sojin Amurka biyu a Otel din Marriott dake Islamabad a watan Satumba 2008.
Mutuwar Qari Yasin babban koma baya ne ga kungiyar dake bata sunan addinin Islama a cewar sakataren tsaron Amurka Jim Mattis .