Pars Today
A Afganistan, mutum 16 ne aka tabbatar da cewa sun rasa rayukansu, sakamakon wasu jerin hare haren kunar bakin wake da musayar wuta da aka kai a wani kamfani na kasar a kusa da filin jirgin sama na Jalalabad dake gabashin kasar.
Kungiyar taliban ta dauki alhakin kai wani hari da yayi sanadin mutuwar mutum 65, a wata cibiyar horon jami'an leken asiri dake lardin Wardak a kudancin kasar ta Afganistan.
Wani sojan kasar Afganistann ya kashe abokan aikisa 8 , ya kona gawakinsu sannan ya kwashe makamansu ya koma cikin mayakan Taliban.
Hukumar zabe a Afganistan, ta sanar da dage zaben shugaban kasar da watanni uku.
An fara tattaunawa mai muhimmanci tsakanin Amurka da kuma kungiyar Taliban ta kasar Afganistan a Hadaddiyar daular Larabawa a jiya Lahadi.
Kungiyar tsaro ta NATO ta sanar da shirinta na tattaunawa da kasar Rasha dangane da rikicin da ya kunno kai tsakanin Rashan da kasar Ukraine cikin kwanakin nan.
Kungiyar Taliban ta dauki alhakin kai harin bam din da ya hallaka wasu sojin Amurka uku a birnin Ghazni dake tsakiyar kasar Afganistan.
Hukumomi a yammacin Afganistan sun sanar da mutuwar 'yan sanda 22 a wani farmaki da 'yan ta'adda Taliban suka kai a yankin farah.
Jiragen saman yakin rundunar sojin Afganistan sun kaddamar da hare-hare kan sansanin mayakan kungiyar Taliban da ke lardin Helmand a shiyar kudancin kasar.
Yau Juma'a, kasar Rasha na karbar batuncin wani taron kasa da kasa kan samar da zaman lafiya a kasar Afganistan.