Dec 03, 2018 16:20 UTC
  • Kungiyar NATO Ta Sanar Da Shirinta Na Tattaunawa Da Rasha Kan Rikicin Ukraine

Kungiyar tsaro ta NATO ta sanar da shirinta na tattaunawa da kasar Rasha dangane da rikicin da ya kunno kai tsakanin Rashan da kasar Ukraine cikin kwanakin nan.

Babban sakataren kungiyar ta NATO, Jens Stoltenberg, ya bayyana hakan a wata ganawa da yayi da manema labarai a yau din nan Litinin a birnin Brussels inda ya ce duk da cewa kungiyar ta NATO da kasashe membobinta suna goyon bayan kasar Ukraine kan rikicin da ya kunno kai tsakaninta da Rasha, to amma a shirye su ke su tattauna da Rashan don kawo karshen rikicin.

Har ila yau babban sakataren kungiyar ta NATO ya kirayi kasar Rashan da ta sako jiragen ruwan Ukraine da matukansu da suke tsare da su sannan kuma ta girmama hurumin kasar Ukraine din.

A ranar Lahadin data gabata ce kasar Rasha ta kame wasu jiragen ruwa uku mallakar kasar Ukraine bisa zargin su da tsallakawa iyakar ruwan kasar lamarin da ya sake tayar da tsohon rikicin da ke tsakanin kasashen biyu.

Tags