Mar 06, 2019 13:26 UTC
  • Hare-haren Kunar Bakin Wake Sunyi Ajalin Mutum 16 A Afganistan

A Afganistan, mutum 16 ne aka tabbatar da cewa sun rasa rayukansu, sakamakon wasu jerin hare haren kunar bakin wake da musayar wuta da aka kai a wani kamfani na kasar a kusa da filin jirgin sama na Jalalabad dake gabashin kasar.

Dukkan wadanda harin ya rusa dasu ma'aikatan kamfanin ne na Entire Builders Engineering (eBe).

Da yake sanar da hakan kakakin gwamnatin Lardin Nangarhar, Attaullah Khogyani, ya ce an kawo karshen harin, wanda aka kai a safiyar yau Laraba, wanda a yayinsa kuma aka hallaka dukkan maharan su guda biyar.

Bayan harin an kuma gano wata mota dake makare da boma-bomai, da rugunan boma bomai da kuma wasu ababe masu fashewa,a cewar Mista Khogyani.

Babu dai wata kungiya data dau alhakin kai harin, a yayin da kungiyar taliban ta nisanta kanta da kai harin, a daidai lokacin da take kan tattaunar zaman lafiya da Amurka.

 

 

Tags