Rasha : Ana Taro Kan Samar Da Zaman Lafiya A Afganistan
(last modified Fri, 09 Nov 2018 09:46:41 GMT )
Nov 09, 2018 09:46 UTC
  • Rasha : Ana Taro Kan Samar Da Zaman Lafiya A Afganistan

Yau Juma'a, kasar Rasha na karbar batuncin wani taron kasa da kasa kan samar da zaman lafiya a kasar Afganistan.

Manufar taron ita ce samar da wata hanyar tattaunawa kai tsaye tsakanin mahukuntan Kabul da kuma kungiyar Taliban.

Wannan dai shi ne karon farko da wani taron kasa da kasa ke samun halartar kungiyar Taliban.

Rasha ta kuma gayyaci kasashen Amurka, Indiya, Iran, China, da Pakistan da wasu kasashen Asiya ta tsakiya a taron.