Yakin Afganistan: Amurka Da Taliban Sun Fara Tattaunawa Mai Muhimmanci
(last modified Mon, 17 Dec 2018 19:15:59 GMT )
Dec 17, 2018 19:15 UTC
  • Yakin Afganistan: Amurka Da Taliban Sun Fara Tattaunawa Mai Muhimmanci

An fara tattaunawa mai muhimmanci tsakanin Amurka da kuma kungiyar Taliban ta kasar Afganistan a Hadaddiyar daular Larabawa a jiya Lahadi.

Kamfanin dillancin labaran Nageria NAN ya nakalto Zabihullah Mujahid kakakin kungiyar Taliban yana fadat haka ba tare da wani karin bayani ba. Labarin ya kara da cewa Khalil Minawi shugaban kamfanin dillancin labaran Bakhtar na gwamnatin kasar Afganistan ya tabbatar da Labarin a shafinsa na tweeter. Ya kuma kara da cewa jami'an gwamnatin Amurka, da na Afganistan, da Pakistan duk sun sami halattan taro na jiya Lahadi.

Kungiyar Taliban ta ki amincewa da tattaunawa kai tsaye da gwamnatin kasar Afganistan don abinda ta kira ""yar Koren Amurkane". 

Majiyar gwamnatin Amurka ta bayyana cewa gwamnatin kasar ta kashe fiye da dalar Amurka Triliyon guda tun lokacinda ta mamaye kasar ta Afganistan a shekara 2001. 

Sannan gwamnatin shugaban Trump tana zargin gwamnatin Pakistan da rashin tabuka wani abin a zo a gani kan tabbatar da zaman lafiya a kasar ta Afganistan duk tare da kudade masu yawa wanda gwamnatin kasar take karba a ko wani shekara.