-
Jami'an Tsaron Labanon Gano Wata Cibiyar 'Yan Ta'adda Mai Hatsarin Gaske A Kasar
Apr 10, 2016 00:04Rahotanni daga kasar Labanon sun bayyana cewar jami'an tsaron kasar sun sami nasarar ganowa da kuma cafke 'yan wata kungiyar 'yan ta'adda mai hatsarin gaske a kasar.
-
Gwamnatin Belgium Ta Sanar Da Ci Gaba Da Tsaurara Matakan Tsaro A Kasar
Apr 09, 2016 23:35Firayi ministan kasar Belgium ya sanar da cewa gwamnatin kasar za ta ci gaba da tsaurara matakan tsaro da zama cikin halin ko ta kwana duk kuwa da kame wani adadi na wadanda ake zargi da hannu cikin harin ta'addancin da aka kai wa kasar kwanakin baya.
-
Ministan Tsaron Iran Ya Kirayi Gwamnatin Amurka Da Ta Daina Goyon Bayan Ayyukan Ta'addanci
Apr 09, 2016 23:24Jamhuriyar Musulunci ta Iran ta yi watsi da zargin sakataren harkokin wajen Amurka John Kerry na cewa tana barazana ga tsaron yankin Gabas ta tsakiya tana mai cewa wajibi ne Amurka ta daina goyon bayan kungiyoyin 'yan ta'adda sannan kuma ta fice daga yanki matukar dai tana son taimakon tsaron yankin ne.
-
Jami'an Tsaron Belgium Sun Kama Wasu Da Ake Zargi Da Harin Ta'addancin Brussels
Apr 08, 2016 12:56Babban mai shigar da kara a kasar Belgium ya sanar da cewa jami'an tsaron kasar sun sami nasarar kame wasu mutane da ake zargi da hannu cikin harin ta'addancin da aka kai birnin Brussels a kwanakin baya.
-
Jami'an Tsaron Pakistan Na Ci Gaba Da Neman Wadanda Suka Kai Harin Lahore
Mar 29, 2016 00:36Gwamnatin kasar Pakistan ta sanar da shirinta da dirar mikiya a kan kungiyoyi masu tsaurin ra'ayin addini musamman a lardin Punjab bayan harin ta'addancin da aka kai wani wajen wasa a garin Lahore, babban birnin lardin a ranar Lahadin da ta gabata, inda ta ce jami'an tsaron kasar na ci gaba da farautar mutanen da suka kai harin.
-
Jami'an Tsaron Pakistan Na Ci Gaba Da Neman Wadanda Suka Kai Harin Lahore
Mar 29, 2016 00:00Gwamnatin kasar Pakistan ta sanar da shirinta da dirar mikiya a kan kungiyoyi masu tsaurin ra'ayin addini musamman a lardin Punjab bayan harin ta'addancin da aka kai wani wajen wasa a garin Lahore, babban birnin lardin a ranar Lahadin da ta gabata, inda ta ce jami'an tsaron kasar na ci gaba da farautar mutanen da suka kai harin.
-
Kamaru: Ana Gudanar Da Binciken Lafiya 'Yar Kunar Bakin Waken Da Tace Tana Daga Cikin 'Yan Chibok
Mar 28, 2016 23:23Hukumomi a kasar Kamaru sun fara gudanar da bincike na likitanci da kuma ba da magani ga 'yar kunar bakin waken nan da jami'an tsaron kasar suka kama a kwanakin baya wacce kuma ta yi ikararin cewa tana daga cikin 'yan makarantar sakandaren garin Chibok da 'yan kungiyar Boko Haram suka sace kimanin shekaru biyu da suka gabata.
-
An Bude Taron Hadin Gwiwa Na Kasashen Larabawa Da Afirka Kan Ta'addanci
Mar 25, 2016 00:59A jiya Alhamis ne aka bude taron ministocin kasashen Larabawa da Afirka su 27 a wajen shakatawar nan na Sharm el-Sheik da ke kasar Masar da nufin karfafa aiki tare a bangaren tsaro da nufin fada da ayyukan ta'addanci.
-
Helkwatar Sojin Nijeriya Ta Mayar Da Martani Ga Sabon Faifan Bidiyon Shekau
Mar 24, 2016 23:32Helkwatar tsaron Nijeriya ta yi watsi da sabon faifai bidiyon da shugaban kungiyar Boko Haram Abubakar Shekau ya fitar inda ta ce za ta ci gaba da kai hare-haren da take kai wa 'yan kungiyar da nufin ganin bayansu duk kuwa da halin damuwar da Shekau din ya nuna yana ciki a sabon faifan bidiyon.
-
Hukumomin Belgium Sun Sanar Da Gano Wadanda Suka Kai Harin Brussels
Mar 23, 2016 05:57Kafafen watsa labaran kasar Belgium sun sanar da cewa jami'an tsaron kasar sun sami nasarar kama mutum na uku da ake zargi da hannu cikin harin ta'addancin da aka kai babban filin jirgin saman Zaventum da ke birnin Brussels na Belgium da kuma wata tashar jiragen kasa a jiya bayan sun gano mutane biyun da suka kai harin.