Hukumomin Belgium Sun Sanar Da Gano Wadanda Suka Kai Harin Brussels
Kafafen watsa labaran kasar Belgium sun sanar da cewa jami'an tsaron kasar sun sami nasarar kama mutum na uku da ake zargi da hannu cikin harin ta'addancin da aka kai babban filin jirgin saman Zaventum da ke birnin Brussels na Belgium da kuma wata tashar jiragen kasa a jiya bayan sun gano mutane biyun da suka kai harin.
A wata sanarwa da kafar watsa labaran kasar ta Belgium ta fitar ta ce mutane biyun farko din da aka gano su wadanda kuma 'yan uwan juna ne su ne Khalid da Ibrahim el-Bakraoui wadanda tun da jimawa 'yan sandan kasar sun san da zamansu da kuma sanya ido kansu.
Bayan wancan sanarwar dai, jami'an tsaron sun sanar da cewa suna neman mutum na uku da ake zargi da hannu cikin harin wanda na'ura ta dauki hotonsa a filin jirgin sama, inda dazu dazun nan suka sanar da samun nasarar kama shi.
Rahotanni daga kasar dai sun ce akalla mutane 34 ne suka mutu sannan wasu kimanin 240 suka samu raunuka wasu kuma masu tsanani sakamakon fashewar bama-bamai guda biyu a filin jirgin sama da tashar jirgin kasa na Brussels a jiya Talata.