Pars Today
Gwamnatin kasar Belgium ta sanar da cewa ta kara daga wakilcin diflomasiyyar Palastine a kasarta zuwa jakadanci mai mainakon wakilci.
Tarayyar turai ta bada sanarwar cewa zata kakaba takunkumi kan duk wani kamfanin kasashen tarayyar da ya dakatar da huldar kasuwanci da Iran don biyayya ga Amurka.
Gwamnatin Demokradiyyar Kongo ta bukaci gwamnatin kasar Belgium da ta rufe karamin ofishin jakadancinta da ke kasar da kuma rage irin zirga-zirgan da kamfanin jiragen samar kasar yake yi zuwa kasar Kongo, a wani abu da ake ganinsa a matsayin ci gaba da kai ruwa rana da ke gudana tsakanin kasashen biyu.
Kasar Belgium ta sanar da shirinta na gabatar da tallafin kudade euro miliyan 25 ga Jamhuriyar Dimakoradiyyar Congo duk da kiran da wasu kungiyoyin kasa da kasa ke yi na kakaba takunkumi kan kasar ta Dimokaradiyyar Congo.
Gwamnatin Belgium ta sanar da cewar ta dakatar da ayyukanta a Jamhuriyar Dimokaradiyyar Congo tare da yanke duk wata alakar taimakekkeniya da mahukuntan kasar.
Daruruwan mutanan birnin Kinshasa ne suka gudanar da zanga-zangar nuna rashin amincewar su da bude sabon ofishin jakadancin kasar Belgium a kasar ta Congo.
Tsohon shugaban yankin catalonia na kasar Spaniya tare da wasu manbobin tsohuwar gwamnatin biyar sun gudu zuwa birnin Brussels na kasar Belgium.
Shugaban Majalisar Shawarar Musulunci ta Iran ya jaddada cewa; Yaki da ta'adda da nufin kawo karshensa yana bukatar samun hadin kan kasashen duniya.
Shugaban kasar Amurka Donal Trump da tokororinsa na kungiyar G7 Ta Kasashe mafi karfin tattalin arziki a duniya sun fara taro a birnin Sicily na kasar Italia a yau Jumma'a kuma tun jiya sabani ya fara bayyana a tsakaninsu kan matsaloli da dama.
Dubun-dubar jama'a ne suke gudanar da gangami da zanga-zanga a birnin Brussels da ma wasu biranan kasar Belgium, inda suke la'antar shugaban Amurka Donald Trump, tare da nuna rashin amincewarsu da zuwansa a kasarsu.