An Gudanar Da Zanga-Zangar Kin Jinin Belgium A D/Congo
Daruruwan mutanan birnin Kinshasa ne suka gudanar da zanga-zangar nuna rashin amincewar su da bude sabon ofishin jakadancin kasar Belgium a kasar ta Congo.
Gidan radion kasa da kasa na Faransa ya nakalto mahalarta zanga-zangar na rera taken rashin amincewa da halartar ministan harakokin wajen Belgium a wurin bude sabon ofishin jakadancin kasar a birnin Kinshasa tare kuma da rera taken yin alawadai ga kasar ta Belgium.
A nasu bangare, hukumomin birnin na Kinshasa ba su halarci bikin bude sabon ofishin jakadancin kasar ta Belgium da aka yi ba, tare da nuna rashin amincewarsu kan halartar ministan harakokin wajen kasar Didier Reynders.
A ranar Litinin din da ta gabata ce ministan harakokin wajen Belgium din ya isa birnin Kinshasa domin halartar bikin bude sabon ofishin jakadancin kasar , a ranar 30 ga watan yuni 1960, jamhuriya demokaradiyar congo ta samu 'yancin kai daga kasar ta Belgium.