Belgium Ta Mayar Da Huldarta Da Palastine Zuwa Jakadanci Maimakon Wakilci
Gwamnatin kasar Belgium ta sanar da cewa ta kara daga wakilcin diflomasiyyar Palastine a kasarta zuwa jakadanci mai mainakon wakilci.
kamfanin dillancin labaran Anadol ya bayar da rahoton cewa, Didier Reynders ministan harkokin wajen kasar Belgium, bayan wata ganawa da ya yi da takwaransa na Palastine Riyad Maliki ya bayyana cewa, kasarsa ta kara daga wakilcin diflomasiyyar Palastine.
Ya ce wannan mataki na zuwa ne bayan gudanar da wata tattaunawa tare da manyan jami'ai na majlaisar dinkin duniya, ta yadda a halin yanzu Palastinu za ta kara yawan jami'an diflomasiyyarta, kuma za su samu wasu Karin abubuwan da ba su da su a lokutan baya ta fuskar diflomasiyya.
Abdulkarim Alfarra wakilin Palastine a kasar Belgium ya bayyana cewa,a halin yanzu kasar ta Belgium ta dauki matakin bayar da dama ga Palastine da ta turo jakada maimakon wakili, kuma ta bude ofishin jakadanci maimakon ofishin wakilci.