Shugaban Yankin Catalonia Yayi Hijra Zuwa Birnin Brussels
(last modified Tue, 31 Oct 2017 06:47:40 GMT )
Oct 31, 2017 06:47 UTC
  • Shugaban Yankin Catalonia Yayi Hijra Zuwa Birnin Brussels

Tsohon shugaban yankin catalonia na kasar Spaniya tare da wasu manbobin tsohuwar gwamnatin biyar sun gudu zuwa birnin Brussels na kasar Belgium.

Jim kadan bayan da babbar kotun kasar Spaniya ta zargi gwamnatin Catalonia da tawaye tare da barnata dukiyar al'ummar, a daren jiya litinin, tsohon shugban yankin na Catalonia Carles Puigdemont tare da wasu mambobin gwamnatinsa biyar sun yi hijra zuwa Brussels babban birnin kasar Belgium inda suka nemi mafukar siyasa a can.

Rahoton ya ce mambobin tsohuwar gwamnatin ta Catalonia da suka gudu tare da tsohon shugaban yankin sun hada da saktarorin dake kula da ma'aikatun cikin gida, kiyon lafiya, tsaro, ayyuka da zamtakewa gami da na harakokin noma da kiwo.

Wannan hijra na zuwa ne bayan da ministan dake kula da 'yan gudun hijra na kasar Belgium a ranar lahadin da ta gabata ya bayyana cewa kasar sa za ta baiwa mambobin tsohuwar gwamnatin ta Catalonia mafaka matukar dai sun bukaci hakan, saidai jim kadan bayan wannan sanarwa piraministan kasar Charles Michel yayi watsi da wannan furuci.

A daren juma'ar da ta gabata ce, piraministan Spaniya Mariano Rajoy ya sanar da rushe gwamnatin yankin Catalonia jim kadan bayan da majalisar dokokin kasar ta amince ma gwamnatin da ta karbe ragamar jagorancin yankin na Catalonia.