Pars Today
Kungiyar 'yan ta'adda ta (IS) ta dauki alhakin kai harin kunan bakin wake da ta ce ya yi sanadin mutuwar mutum a kalla 15 a babban ofishin hukumar zabe na Tripoli.
Hukumomin kiwan lafiya a Afganistan sun ce a kalla mutane 31 ne suka rasa rayukansu, kana wasu 54 na daban suka raunana, biyo bayan wani harin kunar bakin wake a kabul, babban birnin kasar.
Kotu a kasar Senegal ta yanke hukuncin daurin shekaru 15 a kidan kaso kan ga wani dan kasar mai dauke da takardar zama dan kasar Faransa bayan da ta same shi da lafin alaka da kungiyoyin 'yan ta'adda.
Wata kotu a kasar Senegal ta zartar da hukuncin dauri na tsawon shekaru 15 a gidan kurkuku kan wani dan kasar da ke da takardar dan kasa a Faransa bayan samunsa da laifin shiga kungiyar ta'addanci.
'Yan sanda a kasar Kenya sun sanya ladan dalar Amurka 160,000 ga duk wanda ya bayar da bayyanan da zasu kai ga cafke wasu 'yan ta'adda takwas da suke nema ruwa a jallo.
Hukumomi a Somaliya sun ce mutane a kalla 14 ne suka gamu da ajalinsu, kana wasu da dama suka raunana a wani harin bam da aka kai a gaban wani shahararren hotel a Mogadisho babban birnin kasar.
Rahotanni daga Afganistan na cewa mutane a kalla 26 ne galibi samari suka rasa rayukansu a wani harin kunar bakin wake da kungiyar 'yan ta'adda ta IS ta dauki alhakin kaiwa a Kabul babban birnin kasar.
Rundunar tsaron Jamhuriyar Musulunci ta Iran ta kame wani gungun 'yan ta'adda a lardin Khuzestan da ke shiyar kudu maso yammacin kasar.
Kungiyar Taliban ta dauki alhakin harin bama-baman da aka kaddamar a birnin kabul fadar mulkin kasar Afghanistan.
Kasashen Iran, Iraki, Siriya Da Rasha sun bayyana wajibcin karfafa cibiyar hadin gwiwa a tsakaninsu da ke birnin Bagadaza da nufin kawo karshen ayyukan ta'addanci a yankin Gabas ta tsakiya.