Taliban Ta Dauki Nauyin Harin Da Aka Kai A Kabul
https://parstoday.ir/ha/news/world-i29171-taliban_ta_dauki_nauyin_harin_da_aka_kai_a_kabul
Kungiyar Taliban ta dauki alhakin harin bama-baman da aka kaddamar a birnin kabul fadar mulkin kasar Afghanistan.
(last modified 2018-08-22T11:31:34+00:00 )
Mar 17, 2018 19:26 UTC
  • Taliban Ta Dauki Nauyin Harin Da Aka Kai A Kabul

Kungiyar Taliban ta dauki alhakin harin bama-baman da aka kaddamar a birnin kabul fadar mulkin kasar Afghanistan.

Kamfadilalncin labaran Shuruq ya bayar da rahoton cewa, zabihullah Mujahid kakakin kungiyar taliban ya bayyana cewa su ne suka kaddamar da harin bama-bamai a birnin Kabul.

Kafin wanann lokacin dai kakain ma'aikatar harkokin cikin gida a kasar Afhhanistan Nusrat Rahimi ya sanar da kai harin, duk da cewa bai tabbatar da wanda suka kai harin ba, amma ya ce ana zargin kungiyar ta Taliban da hannu a harin.

An kai harin ne dai da wata mota da aka shakare da bama-bamai a jiya a cikin birnin kabul, wanda ya nufi wasu sojojin Birtaniya, amma a cewar mahukuntan Afghanistan harin bai same su ba, amma dai wasu fararen hula biyar sun rasa rayukansu, wasu kuma sun jikkata.