Pars Today
Majalisar Dinkin Duniya, ta ce tana ci gaba da tattaunawa domin kaucewa zubar da jini a birnin Hodeida na kasar Yemen, inda kawancen da Saudiyya ke jagoranta ya kaddamar da hari a yau Laraba.
Asusu kula da kananan yara na Majalisar Dinkin Duniya "UNICEF" ya sanar da cewa: Kananan yara miliyan 11 ne suke bukatar agajin gaggawa a Yamen sakamakon yakin da ke faruwa a kasar.
Babban sakataren Jam'iyyar Popular Congress Party ta kasar Sudan ya jaddada yin kira ga gwamnatin Sudan kan hanzarta ficewa daga cikin rundunar hadin gwiwar Saudiyya da take yaki a kasar Yamen.
Jiragen saman yakin masarautar Saudiyya sun yi luguden wuta kan yankunan lardin Hajjah da ke arewa maso yammacin kasar Yamen.
Kawancin kasar Saudia wadanda suke yakar kasar Yemen sun bukaci taimakon Amurka don kwace iko da birnin Hudaida na bakin ruwa a kasar ta Yemen.
Majiyar asibitin Yamen ta sanar da cewa: Jiragen saman yakin masarautar Saudiyya sun yi luguden wuta kan gidajen fararen hula a lardin Sa'adah da ke arewacin kasar lamarin da ya janyo hasarar rayukan mutane akalla 9.
Shugaban kungiyar Ansarullah ta kasar Yemen Abdul Malik Badruddin Al-huthi ya bayyana cewa an ga jiragen yakin HKI suna shawagi a kan garin Hudaida na bakin ruwa a kasar ta Yemen a cikin yan kwanakin da suka gabata.
Wasu jerin hare-hare da sojojin Yamen da dakarun sa-kai da suke rufa musu baya suka kaddamar kan sojojin hayar Saudiyya sun kashe da dama daga cikinsu.
Saudiyya ta sanar da cewa wasu sojojin kasar sun mutu a wani gumurzu da suka yi da dakarun kungiyar Ansarullah na kasar Yemen a kan iyakar Saudiyya da Yemen din.
Dakarun kasar Yemen tare da daukin dakarun sa kai na kasar sun kai wani hari kan sansanin sojin kasar Saudiyya da ke Najran da ke kudancin kasar Saudiyyan a matsayin mayar da martani ga ci gaba da har-haren wuce gona da iri da Saudiyyan da kawayenta suke kai wa al'ummar Yemen.