UNICEF: Yara Miliyan 11 Ne Ke Bukatar Agaji A Kasar Yamen
Asusu kula da kananan yara na Majalisar Dinkin Duniya "UNICEF" ya sanar da cewa: Kananan yara miliyan 11 ne suke bukatar agajin gaggawa a Yamen sakamakon yakin da ke faruwa a kasar.
Asusun kula da kananan yara na Majalisar Dinkin Duniya "UNICEF" ya fayyace cewa: Hare-haren wuce gona da iri da rundunar kawancen masarautar Saudiyya ke ci gaba da kaddamarwa a kasar Yamen Yamen sun wurga rayuwar al'ummar kasar cikin mawuyancin hali, inda a halin yanzu akwai kananan yara miliyan 11 da suke bukatar tallafin gaggawa a sassa daban daban na kasar.
Asusun na "UNICEF" ya kara da cewa: A halin yanzu akwai kananan yara kimanin 300,000 a garin Hadidah da kewaye da suke cikin halin kaka-ni ka yi sakamakon matakin da rundunar kawancen Saudiyya suka dauka na yin kawanya wa garin a kokarin da suke yi na kwace iko da shi.