Kira Ga Gwamnatin Sudan Kan Hanzarta Ficewa Daga Rundunar Hadin Guiwar Saudiyya
Babban sakataren Jam'iyyar Popular Congress Party ta kasar Sudan ya jaddada yin kira ga gwamnatin Sudan kan hanzarta ficewa daga cikin rundunar hadin gwiwar Saudiyya da take yaki a kasar Yamen.
A taron manema labarai da ya gudanar a birnin Khartum fadar mulkin kasar Sudan: Babban sakataren Jam'iyyar Popular Congress Party ta kasar Sudan Ali Al-Hajj ya bayyana cewa: Al'ummar Sudan suna bukatar ganin gwamnatin kasar ta hanzarta janye sojojinta daga cikin kawancen masarautar Saudiyya da suke yaki a kasar Yamen.
Ali Al-Hajj ya kara da jaddada tsananin damuwarsa kan yadda tashe-tashen hankula suke ci gaba da wanzuwa a kasashen Larabawa musamman Siriya, Iraki da Yamen tare da bayyana takaicinsa kan yadda al'ummar Larabawa da kanta take kokarin rusa kanta ta hanyar daukan matakin soji kan makobciyarta.