-
An Yi Alkawarin Bayar Da Taimakon Kudade Ga Kasashen Da Boko Haram Ta Addaba
Sep 04, 2018 07:58Gwamnatin kasar Jamus ta yi alkwarin bayar da wasu makudaden kudade a matsayin tallafi ga kasashen da Boko Haram ta addaba.
-
Wata Babbar Kotu A Kongo Ta Hana Shugaban Wata Jam'iyyar Adawa Shiga Takarar Neman Shugabancin Kasar
Sep 04, 2018 02:04Kotun kundin tsarin mulki a kasar Kongo Kinsasha ta hana shugaban wata jam'iyyar adawar kasar shiga takarar shugabancin kasar
-
Mutane 8 Ne Suka Rasa Rayukansu Sanadiyyar Fashewar Abubuawa A Wani Kamfani A Kasar Afrika Ta Kudu.
Sep 04, 2018 02:03Fashewar wasu abubuwa a wani kamfanin karafa a kasar Afrika ta kudu ya yi sanadiyyar mutuwar mutane akalla 8.
-
Yawan Wadanda Suke Mutuwa Sanadiyar Cutar Ebola A Kasar Congo Yana Karuwa
Sep 04, 2018 02:02Ma'aikatar lafiya ta kasar Democradiyyar Kongo ta bada sanarwan cewa yawan mutanen da suke mutuwa sanadiyyar cutar Ebola a wannan karon ya kai mutane 75.
-
Najeriya: An Sami Karuwar Sojojin Da Boko Haram Su Ka Kashe
Sep 03, 2018 14:32Majiyar sojan Najeriya ce ta sanar da karuwar wadanda su ka kwanta dama sanadiyyar harin na 'yan ta'addar Boko Haram akan iyaka da kasar Nijar.
-
Congo: 'Yan Adawa Sun Fifita Yin Amfani Da Takardu A Zabe Maimakon Na'ura
Sep 03, 2018 14:31Jam'iyyun hamayya da kungiyoyin fararen hula sun yi kira da a yi amfani da takardu a yayin zaben shugaban kasa maimakon amfani da na'ura.
-
MDD Ta Bai Wa Kasar Tanzania Tallafin Kudade
Sep 03, 2018 14:29Shugaban hukumar abinci ta duniya a kasar Tanzania ne ya sanar da ba da kudaden da su ka kai dalar Amurka miliyan 4 domin fada da yunwa
-
An Sanya Dokar Ta Bace A Libiya
Sep 03, 2018 06:48hukumomin birnin Tripoli sun sanya dokar ta bace sandiyar tashin hanakali da ya auku a birnin
-
Harin Kunar Bakin Wake Ya Hallaka Mutane 6 A Birnin Magadushu.
Sep 03, 2018 06:48Wani Dan kunar bakin wake ya tayar da Bam din dake jikinsa a kusa da wata ma'aikatar Gwamnatin dake Magadushu babban birnin kasar Somaliya lamarin da ya yi sanadiyar mutuwar mutane 6 da kuma jikkata wasu 12 na daban.
-
Fursinoni Kimani 400 Ne Suka Gudu Daga Wani Gidan Yari A Birnin Tripoli Na Kasar Libya
Sep 03, 2018 02:05Fursinoni a gidan yarin Ain Zara a cikin birnin Tripoli na kasar Libya kimani 400 suka fice daga gidan yarin a dai dai lokacinda fada ta barke tsakanin kungiyoyi dauke da makamai a cikin birnin.