MDD Ta Bai Wa Kasar Tanzania Tallafin Kudade
Sep 03, 2018 14:29 UTC
Shugaban hukumar abinci ta duniya a kasar Tanzania ne ya sanar da ba da kudaden da su ka kai dalar Amurka miliyan 4 domin fada da yunwa
Micheal Dunford na hukumar abinci ta duniyar da ke karkashin Majalisar Dinkin Duniya ya sanar da cewa; An ba da taimakon kudaden ne domin fada da yunwa da kuma rashin abinci mai gina jiki.
Dunford ya kara da cewa za a yi amfani da tsare-tsare masu inganci a hannun kwararrun manajoji masu zartarwa domin kawo karshen yunwa da kuma rashin abinci mai gina jiki.
Tun a farkon wannan shekarar ta 2018 ne dai hukumar abinci ta duniyar ta sanar da cewa za ta yi aiki a tare da gwamnatin kasar Tanzania domin samar da lamuni na abinci.