Yawan Wadanda Suke Mutuwa Sanadiyar Cutar Ebola A Kasar Congo Yana Karuwa
https://parstoday.ir/ha/news/africa-i33032-yawan_wadanda_suke_mutuwa_sanadiyar_cutar_ebola_a_kasar_congo_yana_karuwa
Ma'aikatar lafiya ta kasar Democradiyyar Kongo ta bada sanarwan cewa yawan mutanen da suke mutuwa sanadiyyar cutar Ebola a wannan karon ya kai mutane 75.
(last modified 2018-09-04T02:02:20+00:00 )
Sep 04, 2018 02:02 UTC
  • Yawan Wadanda Suke Mutuwa Sanadiyar Cutar Ebola A Kasar Congo Yana Karuwa

Ma'aikatar lafiya ta kasar Democradiyyar Kongo ta bada sanarwan cewa yawan mutanen da suke mutuwa sanadiyyar cutar Ebola a wannan karon ya kai mutane 75.

Majiyar muryar JMI daga birnin Kinshasa ta nakalto rahoton ma'aikatar lafiya na kasar tana fadar haka a jiya Litinin, ta kuma kara da cewa ya zuwa yanzu mutane 111 aka tabbatar da kamuwarsu da wannan cutar sannan mutane 75 daga cikinsu sun rasa rayukansu. 

A ranar 8 ga watan Mayun da ya gabata ne cutar ta bulla a garin Bikoro a cikin lardin Aquateur arewa maso yammacin kasar ta Kongo, sannan ta watsu zuwa garin Mbandaka da ke tsakiyar kasar .

Wannan dai shi ne karo na na ukku kenan cutar Ebola tana bulla a kasar ta Kongo tun shekara ta 2014.