-
Sojojin Masar Sun Kadamar Da farmaki A Garin Rafah
Jul 23, 2018 05:33A wannan Lahadi, dakarun tsaron Masar sun kadamar da gagarimin farmaki a garin Rafah dake jihar Sinai kusa da kan iyakar yankin zirin Gaza na Palastinu.
-
Shugaban China Na Ziyara A Afrika
Jul 23, 2018 05:30A jiya asabar shugaban kasar China Xi Jinping yafara ziyarar aiki na mako guda a wasu kasashen Afira inda ya fara da birnin Dakar na kasar Senegal.
-
Ana Shirin Ayyana Karshen Ebola A DR Congo
Jul 23, 2018 02:44A wani lokaci nan da mako guda ne ake sa ran hukumomi a jamhuriya Demokuradiyyar Congo, zasu sanar da kawo karshen cutar Ebola a yankin Equator dake arewacin kasar.
-
Boko Haram Ta kashe Mutum 18 A Chadi
Jul 23, 2018 02:42Wasu mayaka da ake kyautata zaton 'yan Boko Haram ne sun kashe mutane 18 da kuma yin awan gaba da mata 10, a lardin Dabua na Chadi dake yankin tafkin Chadi.
-
Sojojin Jamhuriyar Niger Sun Kashe 'Yan Ta'addan Kungiyar Boko Haram Masu Yawa
Jul 22, 2018 07:31Ma'aikatar tsaron Jamhuriyar Niger ta sanar da cewa: Sojojin gwamnatin kasar sun yi nasarar halaka mayakan kungiyar Boko Haram akalla 10 a yankin kudu maso gabashin kasar.
-
Wasu 'Yan Bindiga Sun Kai Hari Kan Sojojin Gwamnatin Masar A Yankin Tsibirin Sina Na Kasar
Jul 22, 2018 07:16Wasu gungun 'yan bindiga sun kai harin wuce gona da iri kan rundunar sojin Masar a yankin Sina kusa da kan iyaka da yankin Zirin Gaza na Palasdinu, inda suka kashe soja guda.
-
Eritrea Ta Tura Jakadanta A Karon Farko Zuwa Kasar Ethiopia Tun Shekaru 20 Da Suka Gabata.
Jul 22, 2018 01:55Gwamnatin kasar Eritrea ta bada sanarwan nada sabon jakadan kasar a kasar Ethiopia ko Habasha bayan katse huldan jakadanci na kimanin shekaru 20.
-
Atiku Abubakar Ya Bayyana Anniyarsa Ta Shiga Takarar Shugabancin Kasar Najeriya
Jul 22, 2018 01:50Tsohon mataimakin shugaban kasa a tarayyar Najeriya Alhaji Atiku Abubakar ya bayyana anniyarsa ta shiga takarar shugaban kasa a zabe mai zuwa a karkashin tutar jam'iyyar PDP.
-
Shugaban Kasar China Ya Fara Gudanar Da Ziyarar Aiki A Nahiyar Afrika
Jul 21, 2018 07:48Shugaban kasar China ya fara gudanar da ziyarar aiki a nahiyar Afrika, inda a halin yanzu haka ya isa kasar Senegal.
-
Kungiyar Al-Shabab Ta Somaliya Ta Mamaye Wani Yankin Puntland Mai Ci Kwarya-Kwaryar Gashin Kai
Jul 21, 2018 07:42Kungiyar ta'ddanci ta Al-Shabab ta Somaliya ta mamaye wani yanki mai muhimmanci a Puntland mai cin kwarya-kwaryar gashin kai a kasar ta Somaliya.