Atiku Abubakar Ya Bayyana Anniyarsa Ta Shiga Takarar Shugabancin Kasar Najeriya
Tsohon mataimakin shugaban kasa a tarayyar Najeriya Alhaji Atiku Abubakar ya bayyana anniyarsa ta shiga takarar shugaban kasa a zabe mai zuwa a karkashin tutar jam'iyyar PDP.
Jaridar Primuimtimes ta Najeriya ta bayyana cewa Atiku ya bada wannan sanarwan ne a wani gangami da ya kira a Yola a jiya Asabar, ya kuma kara da cewa idan aka zabe shi zai dawo da zaman lafiya a kasar ya kuma samar da ayyukan yi ga matasa kimani miliyon guda da basa da aikin yi.
A cikin watan Febreru mai zuwa ne ake saran Jam'iyyar ta PDP wacce ita ce jam'iyyar adawa mafi girma a kasar zata gudanar da zaben fidda goni wanda zai tsayawa jam'iyyar takara a zaben shugaban kasa na shekara mai zuwa.
Banda Alhaji Atiku Abubakar, akwai tsohon gwamnan jihar Kaduna Ahmad Makarfi da kuma Alhaji Sule Lamido shima tsohon gwamnan jihar Jigawa da kuma Alhaji Rabiu Musa Kwankwaso na jihar Kano, Aminu Tambuwal na jihar sokokto duk a cikin masu neman takarar shugaban kasa a karkashin jam'iyyar ta PDP.