Ana Shirin Ayyana Karshen Ebola A DR Congo
https://parstoday.ir/ha/news/africa-i32435-ana_shirin_ayyana_karshen_ebola_a_dr_congo
A wani lokaci nan da mako guda ne ake sa ran hukumomi a jamhuriya Demokuradiyyar Congo, zasu sanar da kawo karshen cutar Ebola a yankin Equator dake arewacin kasar.
(last modified 2018-08-22T07:02:08+00:00 )
Jul 23, 2018 02:44 UTC
  • Ana Shirin Ayyana Karshen Ebola A DR Congo

A wani lokaci nan da mako guda ne ake sa ran hukumomi a jamhuriya Demokuradiyyar Congo, zasu sanar da kawo karshen cutar Ebola a yankin Equator dake arewacin kasar.

Wannan dai ya biyo bayan da hukumar lafiya ta Duniya (WHO) ta sanar da cewa ba'a samu wani sabon kamuwa da cutar ba tun daga ranar 12 ga watan Yuni, a Jamhuriya Demokuradiyyar ta Congo ba.

A ranar 25 ne ga watan nan ne ake sa ran hukumomin kasar zasu sanar da kawo karshen cutar a hukumance.

Alkalumman da hukumar lafiyar ta fitar sun nuna cewa mutum 24 ne suka warke dage cutar cikin 53 a wasu sassan kasar uku, a yayin da 29 suka rasa rayukansu.

A karon farko ne dai a kasar akayi amfani da allurar gwajin warkar da cutar ta Ebola a wannan kasa ta DR Congo.