Shugaban China Na Ziyara A Afrika
https://parstoday.ir/ha/news/africa-i32437-shugaban_china_na_ziyara_a_afrika
A jiya asabar shugaban kasar China Xi Jinping yafara ziyarar aiki na mako guda a wasu kasashen Afira inda ya fara da birnin Dakar na kasar Senegal.
(last modified 2018-08-22T07:02:08+00:00 )
Jul 23, 2018 05:30 UTC
  •  Shugaban China Na  Ziyara A Afrika

A jiya asabar shugaban kasar China Xi Jinping yafara ziyarar aiki na mako guda a wasu kasashen Afira inda ya fara da birnin Dakar na kasar Senegal.

Wannan ziyara dai ita ce karo na uku da shugaba  Xi Jinping ke gudanar da ita a  Afirka a matsayinsa na shugaban kasa, inda bayan da ya gana shugaban Macky Sall a birnin Dakar, ya  wuce zuwa birnin Kigali na Rwanda inda zai  gana da shugaba Paul Kagame, sannan  a ranar Laraba ya wuce zuwa Afirka ta Kudu domin halartar taron kasashen duniya masu samun habakar tattalin arziki wato Brics a birnin Johanneshurg.

Ziyarar Xi dai na zuwa ne a daidai lokacin da Chinan ke fuskantar gagarumar hamayya a fannin kasuwanci daga gwamnatin Shugaba Donald Trump na Amirka, wanda gwamnatinsa ba ta damu sosai da kulla alaka da nahiyar ta Afirka ba, yankin da ke zaman na biyu mafi yawan al'umma a duniya.