-
Sojojin Kasar Somaliya Sun Hallaka 'Yan Ta'addan Kungiyar Al-Shabab Su 7
Jun 26, 2018 06:41Sojojin kasar Somaliya sun ba da labarin cewa a wani gumurzu da suka yi da 'yan kungiyar ta'addancin nan ta Al-Shabab a kudancin kasar, sun sami nasarar hallaka 7 daga cikin 'yan ta'addan.
-
Sharhi: Tattaunawar Sulhu Tsakanin Gwamnatin Sudan Ta Kudu Da 'Yan Tawaye
Jun 26, 2018 02:45A daren jiya ne aka fara gudanar da tattaunawar sulhu zagaye na biyu tsakanin gwamnatin kasar Sudan ta kudu da kuma bangaren 'yan tawayen kasar a birnin Khartum fadar mulkin kasar Sudan.
-
Shugabannin 'Yan Sanda Na Kasashen ECOWAS Na Taro Kan Yaki Da Ta'addanci
Jun 26, 2018 01:24Shugabannin 'yan sanda da kuma na tsaro na kasashen mambobin kungiyar raya arzikin kasashen yammacin Afrika ECOWAS/CEDEAO, sun fara wani taron na yini uku a birnin Abidjan na kasar Ivory Coast mai manufar karfafa hadin guiwa don yaki da ta'addanci.
-
Zimbabwe : 2 Daga Cikin Mutane 49 Da Suka Raunana Sun Mutu
Jun 26, 2018 01:21A Zimbabwe, an sanar da mutuwar mutum 2 daga cikin 49 da suka raunana a harin da aka kai a yayin gangamin yakin neman zabe na Shugaban kasar, Emmerson Mnangagwa.
-
Miyatti Allah: Ba Ma Goyon Bayan Kissa Amma Harin Barikin Ladi Ramuwar Gayya Ce
Jun 25, 2018 14:27Kungiyar Miyetti Allah ta Fulani makiyaya ta bayyana cewa kisan mutane akalla 86 da aka yi a ranar Asabar da ta gabata a jihar Plato harin ramuwa ce na hare haren da aka kaiwa wasu Fulani makiya a yankin.
-
Sudan Ta Kudu : Mashar Da Kiir Zasu Gana A Khartum
Jun 25, 2018 06:06Jagoran 'yan adawa a Sudan ta kudu, Riek Mashar, ya isa a birnin Khartoum na Sudan inda yau Litini zai fara wata tattaunawa da shugaba, Salva Kiir na Sudan ta Kudu, kan batutuwan da bangarorin biyu ke takkadama da juna akansu da suka hada da mulki da kuma tsaro.
-
Burkina Faso : Kabore Zai Yi Takara A Zaben 2020
Jun 25, 2018 06:05Shugaba Roch Marc Christian Kabore na Burkina faso , ya bayyana aniyarsa ta sake tsayawa takara a zaben shugabancin kasar na 2020 domin neman wa'adin mulki na biyu.
-
Mali: An Yi Wa Fararen Hula 50 Kisan Kiyashi
Jun 25, 2018 03:44Wasu masu dauke da makamai da ba a tantance su ba, sun kai hari a kauyen Mopti da ke tsakiyar kasar Mali inda su ka kashe mutane 50
-
Sudan Ta Soki Kotun Kasa Da Kasa Ta Manyan Laifuka
Jun 25, 2018 03:35Ma'aikatar harkokin wajen kasar Sudan ta ce; Babu wani sakamako da ya fito daga kwamitin tsaro na MDD Akan rahoton kotun manyan laifuka ta kasa da ka dangane da yankin Darfur,
-
Russia 2018 : Senegal Ta Yi Kunnen Doki Da Japan 2-2
Jun 24, 2018 12:56A ci gaba da gasar cin kofin kwallon kafa na duniya da Rasha ke karbar bakunci, an tashi kunnen doki tsakanin tawagar kwallon kafa ta Senegal da Japon 2-2 a wasaninsu na biyu biyu da suka buga da maraicen yau a rukunin H.