Burkina Faso : Kabore Zai Yi Takara A Zaben 2020
Jun 25, 2018 06:05 UTC
Shugaba Roch Marc Christian Kabore na Burkina faso , ya bayyana aniyarsa ta sake tsayawa takara a zaben shugabancin kasar na 2020 domin neman wa'adin mulki na biyu.
Mista Kabore, ya bayyana cewa, doka ta bashi damar yin wa'adin mulki na biyu, a don haka zai fafatukar ganin ya cimma gurinsa a wannan wa'adin, don neman wani wa'adi na biyu a zaben kasar mai zuwa a 2020.
A jiya Lahadi ne dai shugaban kasar ya yi wa al'ummar kasar jawabi na raskwanar aikin da ya yi a rabin wa'adin mulkinsa na farko.
A watan Nowamba na shekara 2015 ne Mista Kobore ya dare kan karagar mulkin kasar ta Burkina Faso, bayan boren da ya cilasta wa tsohon shugaban kasar Blaise Compaure barin mulki.