Sudan Ta Kudu : Mashar Da Kiir Zasu Gana A Khartum
(last modified Mon, 25 Jun 2018 10:36:18 GMT )
Jun 25, 2018 10:36 UTC
  • Sudan Ta Kudu : Mashar Da Kiir Zasu Gana A Khartum

Jagoran 'yan adawa a Sudan ta kudu, Riek Mashar, ya isa a birnin Khartoum na Sudan inda yau Litini zai fara wata tattaunawa da shugaba, Salva Kiir na Sudan ta Kudu, kan batutuwan da bangarorin biyu ke takkadama da juna akansu da suka hada da mulki da kuma tsaro.

Ko a makon da ya gabata ma dai bangarorin dake gaba da juna sun gana a birnin Adis Ababa na kasar Habasha, a bisa gayyatar fira minsitan Habasha, Abiy Ahmed, bisa matsin lamba na kasa da kasa na ganin an kawo karshen yakin da kasar ta Sudan ta Kudu.

Sudan ta kudu ta fada cikin yakin basasa ne tun a watan Disamba 2013, bayan rikicin da ya barke tsakanin Shugaba Salva Kiir da Riek Mashar wanda shi ne mataimakinsa a lokacin.

Dubban mutane ne suka rasa rayukansu, a yayin da wasu Miliyan hudu suka kaurace wa muhallansu a wannan kasa ta Sudan ta Kudu.