-
Gwamnatin Libiya Da Ke Tabruk Ta Nuna Rashin Amincewarta Da Shawarar Kasar Faransa
May 20, 2018 07:48Kakakin Majalisar Dokokin Libiya da ke da matsuguni a garin Tabruk ya bayyana rashin amincewarsu da shawarar da kasar Faransa ta gabatar a matsayin hanyar warware dambaruwar siyasar kasar.
-
An Samu Bullar Cutar Kwalara A Sansanin 'Yan Gudun Hijira A Kasar Kenya
May 20, 2018 07:46Bullar cutar kwalara a sansanin 'yan gudun hijira na Dadaab da ke kasar Kenya ta lashe rayukan mutane akalla bakwai ciki har da kananan yara.
-
Ma'aikatar Harkokin Wajen Sudan Ta Kirayi Jakadan Masar Domin Bayyana Masa Kokenta
May 20, 2018 07:44Ma'aikatar harkokin wajen Sudan ta kirayi jakadan Masar da ke kasarta domin bayyana masa rashin jin dadinta kan wani wasan kwaikwayo da za a nuna a wata tashar talabiji na kasar Masar.
-
An Sako Kananen Yara Sama Da 200 A Sudan Ta Kudu.
May 20, 2018 03:25MDD ta sanar da cewa 'yan bindiga sun sako kananen yara sama da 200 A kasar Sudan Ta Kudu.
-
'Yan Ta'adda Na Garkuwa Da Mutane A Libiya
May 20, 2018 03:24Hukumomin kasar Libiya sun yi gargadi kan yadda 'yan ta'adda ke amfani da fararen hula domin kare kansu a gabashin kasar
-
An Kashe Mutane 17 A Kauyen Tilabery Dake Kasar Nijer
May 20, 2018 03:23Wasu mahara kan babura dauke da mugan makamai sun kashe Fulani 17 a kauyen Aghay dake Inates yankin Tillabery a Jamhuriyar Nijar da kan iyaka da kasar Mali.
-
An Kama Sama Da Mutane 200 Sakamakon Samamen Fada Da Ta'addanci A Yammacin Afirka
May 19, 2018 13:24Rundunar sojin kasar Burkina Faso ta sanar da cewa an samu nasarar kame sama da mutane 200 a wasu samame na hadin gwiwa tsakanin jami'an tsaron kasashen Burkina Faso, Ghana, Benin da Togo da nufin fada da ta'addanci.
-
Iyalan Tsohon Shugaba Morsi Sun Nuna Tsananin Damuwarsu Kan Halin Da Yake Ciki
May 19, 2018 13:24Iyalan hambararren shugaban kasar Masar Muhammad Morsi sun bayyana tsananin damuwarsu dangane da mawuyacin halin da yake ciki a inda ake tsare da shi.
-
Jami'an Tsaron Moroko Sun Fara Rusa Matsugunun Bakin Haure Da Suke Cikin Kasar
May 19, 2018 07:53Jami'an tsaron Moroko sun fara gudanar da shirin rusa matsugunan da bakin haure suke kafawa a cikin kasar da nufin yada zango kafin samun damar kutsawa cikin kasashen yammacin Turai.
-
M.D.Duniya Ta Nuna Damuwa Kan Matsalar Gudun Hijirar Kasar Afrika Ta Tsakiya
May 19, 2018 07:37Hukumar kolin kula da 'yan gudun hijira ta Majalisar Dinkin Duniya ta bayyana damuwarta kan yadda ake ci gaba da samun kwararar 'yan gudun hijira daga Jamhuriyar Afrika ta Tsakiya zuwa Jamhuriyar Dimokaradiyyar Congo.