M.D.Duniya Ta Nuna Damuwa Kan Matsalar Gudun Hijirar Kasar Afrika Ta Tsakiya
Hukumar kolin kula da 'yan gudun hijira ta Majalisar Dinkin Duniya ta bayyana damuwarta kan yadda ake ci gaba da samun kwararar 'yan gudun hijira daga Jamhuriyar Afrika ta Tsakiya zuwa Jamhuriyar Dimokaradiyyar Congo.
A bayanin da Hukumar kolin kula da 'yan gudun hijira ta Majalisar Dinkin Duniya ta fitar yana dauke da cewa: 'Yan gudun hijirar Jamhuriyar Afrika ta Tsakiya da mafi yawansu mata ne da kananan yara suna ci gaba da kwarara zuwa Jamhuriyar Dimokaradiyyar Congo domin neman mafaka duk kuwa da mummunan halin da Jamhuriyar Dimokaradiyyar Congo take ciki.
Bayanin Hukumar kolin kula da 'yan gudun hijirar ya kara da cewa: A kasa da shekara guda yawan 'yan gudun hijirar Jamhuriyar Afrika ta Tsakiya daga 102, 000 ya haura zuwa 182, 000, kuma ana ci gaba da samun kwararar 'yan gudun hijirar.