An Kashe Mutane 17 A Kauyen Tilabery Dake Kasar Nijer
Wasu mahara kan babura dauke da mugan makamai sun kashe Fulani 17 a kauyen Aghay dake Inates yankin Tillabery a Jamhuriyar Nijar da kan iyaka da kasar Mali.
Kamfanin dillancin labaran kasar Faransa ya habarta cewa a daren juma'ar da ta gabata wasu mutane dauke da makamai kan babura sun kai gari kauyen Aghay na jahar Tilabery mai iyaka da kasar Mali. an kai harin ne a dai dai lokacin da mutane ke shirin shan ruwa kuma wannan mumunan hari ya kara sanya tsoro da fargaba a cikin zukatan al'ummar yankin duk da kokarin da hukumomin suka ce suna yi na tabbatar da tsaro a wadanan yankuna da aka jima ana bayyana su a matsayin wurraren dake tattare da hatsari.
Mazauna yankin da suka hada da Zabarmawa, Fulani da Bugaje na kallon wannan hari a matsayin ramuwar gaya daga bugajen kasar Mali tun bayan wani hari da Fulani mazauna Aghay suka kai musu a ranar 18 ga watan Afrilun da ya gabata inda Fulani suka kashe Bugaje 16.