-
Gwamnatin Nijeriya Ta Biyan Mutane 14 Da Suka Fallasa Mata Barayin Gwamnati Hakkokinsu
May 13, 2018 01:06Gwamnatin tarayyar Nijeriya ta ce ta biya wasu mutane 14 da suka ba ta wasu muhimman bayanai da suka ba ta damar kwato biliyoyin Nairori da kuma wasu miliyoyin na daban cikin kudaden kasashen waje ladar da aka yi musu alkawarin ba su cikin shirin da gwamnatin ta fito da shi na ba da lada ga wadanda suka fallasa mata wadanda suka sace kudin kasar.
-
Mahara Sun Kashe Mutane 26 A Kasar Burundi, Gabannin Zaben Da Za'a Gudanar A Kasar
May 13, 2018 01:02Rahotanni daga kasar Burundi sun bayyana cewar alal akalla mutane 26 sun mutu kana wasu da dama kuma sun sami raunuka sakamakon hari da wasu mahara suka kai lardin Cibitoke da ke arewa masu yammacin kasar.
-
Mutum Guda Ya Mutu Wasu Sun Sami Raunuka Wajen Rantsar Da Sabon Shugaban Saliyo
May 13, 2018 01:02Rahotanni daga kasar Saliyo sun ce alal akalla mutum guda ya mutu kana wasu kimanin 20 kuma sun sami raunuka a lokacin da suke kokarin kutsawa cikin babban filin wasan kwallon kafa na garin Freetown, babban birnin kasar don halartar bikin rantsar da sabon shugaban kasar Julius Maada Bio a jiya Asabar.
-
Burundi: Mutane 26 Sun Hallaka A Arewa Maso Yammacin Kasar
May 12, 2018 14:59A Wani hari da wani gungu masu dauke da makamai suka kai wasu kauyuka na arewa masu yammacin kasar Burindi, kimanin mutane 26 suka rasa rayukansu yayin da wasu 10 na daban suka jikkata
-
MDD Ta Yi Gargadi Kan Take Hakin Bil-Adama A Sudan Ta Kudu
May 12, 2018 14:58Wakilin musaman na MDD a Sudan ta kudu ya yi gargadi kan yadda ake take hakin bil-adama musaman kan cin zarafin diya mata a kasar
-
Congo Brazzaville: An daure dan takarar shugaban kasa zaman kurkuku na shekaru 20
May 12, 2018 07:52Tsohon hafsan hafsoshin sojan kasar Brazzaville kuma dan takarar shugabancin kasar Jean-Marie Michel Mococco ya fuskanci dauri akan yi wa tsaron kasa illa haka nan kuma mallakar makamai ba bisa ka'ida ba
-
Buratai: Dukkan Bangarorin Biyu Suna Da Laifi A Rikicin Jihar Benue
May 12, 2018 04:45Babban hafsan hafsoshin sojojin Nijeriya Janar Tukur Brutai ya bayyana cewa dukkan bangarorin da suke rigima da juna suna da hannu cikin laifuffukan da aka aikata a jahar Benue.
-
'Yan Sanda Sun Kashe Mutane 18 Da Kama Wasu 56 Da Suke Da Hannu Cikin Kashe-Kashen Kaduna, Zamfara
May 11, 2018 13:43Rundunar 'yan sandan jihar Kaduna a Nijeriya sun sanar da hallaka wasu mutane 18 masu dauke da makami da kuma kama wasu 56 da ake zargin suna da hannu cikin kashe-kashe da sace-sacen mutane a karamar hukumar Birnin Gwari na jihar da kuma jihar Zamfara.
-
An Kashe Wani Jami'in Diplomasiyyar Nijeriya A Kasar Sudan
May 11, 2018 13:42Majiyoyin tsaron kasar Sudan sun bayyana cewar wasu mutane da ba a riga da an tantance su ba sun kashe wani jami'in diplomasiyyar Nijeriya a kasar ta Sudan a safiyar yau Alhamis.
-
Hamas: Za A Ci Gaba Da Zanga-Zanga Akan Hakkin Komawar Palasdinawa Zuwa Gidajensu Na Gado
May 11, 2018 07:44Shugaban Kungiyar gwagwarmayar musulunci ta Hamas a yankin Gaza Yahya Sinwar ne ya bayyana cewa Za a ci gaba da zanga-zangar har zuwa lokacin da za a kai ga cimma manufa.