Buratai: Dukkan Bangarorin Biyu Suna Da Laifi A Rikicin Jihar Benue
https://parstoday.ir/ha/news/africa-i30742-buratai_dukkan_bangarorin_biyu_suna_da_laifi_a_rikicin_jihar_benue
Babban hafsan hafsoshin sojojin Nijeriya Janar Tukur Brutai ya bayyana cewa dukkan bangarorin da suke rigima da juna suna da hannu cikin laifuffukan da aka aikata a jahar Benue.
(last modified 2018-08-22T07:01:49+00:00 )
May 12, 2018 04:45 UTC
  • Buratai: Dukkan Bangarorin Biyu Suna Da Laifi A Rikicin Jihar Benue

Babban hafsan hafsoshin sojojin Nijeriya Janar Tukur Brutai ya bayyana cewa dukkan bangarorin da suke rigima da juna suna da hannu cikin laifuffukan da aka aikata a jahar Benue.

Tukur Brutai ya bayyana haka ne a wata hirar da ta hada shi da Jaridar DailyTrust ta Nigeria. Shugaban sojojin ya kara da cewa mutane kasar Benue da kuma Makiyaya duk suna da hannu wajen tada zaune tsaye a jihar, kuma sojojinsa suna samun nasara a kansu.

Dangane da irin ci gaban da aka samu wajen tabbatar da zaman lafiya da tsaro a jihar Benue shugaban Sojojin ya ce sojojinsa sun dawo da zaman lafiya a yankuna masu yawa a jihar Benue, ya kuma yi kira ga wadanda suka kauracewa gidajensu a wadannan yankuna da cewa suna iya komawa gidajensu.

A makon da ya gabata ne Janar Tukur Brutai ya kai ziyarar ganin Ido zuwa jihar Benue wacce tayi ta fama da rikice-rikicen kabilanci tsakanin fulani makiya da kuma yan kabilar tibi manoma.