May 11, 2018 12:14 UTC
  • Hamas: Za A Ci Gaba Da Zanga-Zanga Akan Hakkin Komawar Palasdinawa Zuwa Gidajensu Na Gado

Shugaban Kungiyar gwagwarmayar musulunci ta Hamas a yankin Gaza Yahya Sinwar ne ya bayyana cewa Za a ci gaba da zanga-zangar har zuwa lokacin da za a kai ga cimma manufa.

Sinwar ya ci gaba da cewa; Killace yankin Gaza da aka yi zalunci ne wanda ya zama wajibi ya zo karshe.

Kungiyar ta Hamas ta fitar da sanarwa ne a jiya alhamis inda ta bukaci fitowar palasdinawa a yau juma'a domin ci gaba da gudanar da gangami a bakin iyakar Gaza da palasdinau da ke karkashin mamaya.

Tun a ranar 30 ga watan Maris ne dai Palasdinawan suka fara gudanar da gangami da zanga-zangar ranar "Hakkin komawa zuwa gida' ta shekara-shekara. Daga lokacin zuwa yanzu Palasdinawa 53 ne su ka yi shahada, kuma wasu fiye da 8500 su ka jikkata.

Tags