-
DRC : Adadin Mutanen Da Suka Kamu Da Cutar Ebola Ya Kai 11
May 11, 2018 01:23Hukumomin kiwan lafiya a Jamhuriya Demokuradiyyar Kango sun ce adadin mutanen da aka tabbatar sun kamu da cutar Ebola a kasar ya karu zuwa goma sha daya.
-
Afrika Ta Kudu : An Kai Harin Wuka Kan Wani Masallacin 'Yan Shi'a
May 10, 2018 23:54Wasu mahara dauke wukake sun farma wa wani masallacin 'yan shi'a a yankin KwaZulu-Natal dake Afrika ta Kudu, inda suka kashe limanim masallacin tare da raunana mutum biyu.
-
Nijar Ta Tisa Keyar 'Yan Sudan 140 Zuwa Libiya
May 10, 2018 23:02Hukumomi a jihar Agadas dake arewacin jamhuriya Nijar, sun tisa keyar 'yan gundun hijira Sudan 140 zuwa yankin Madama a iyaka da Libiya, bisa dalilai na tsaro.
-
Sojojin Masar Sun Halaka 'Yan Ta'adda 21 A Yankin Sinai
May 10, 2018 22:09A ci gaba da kaddamar da farmakin da dakarun gwamnatin Masar ke a yankin Sinai, sun sanar da halaka 'yan ta'adda 21 a yankin tare da kame wasu.
-
Sufeto Janar Na 'Yan Sandan Nijeriya Ya Zargin 'Yan Majalisar Kasar Da Kokarin Bata Masa Suna
May 10, 2018 06:09Sufeto Janar na 'yan sandan Nijeriya, Ibrahim Idris ya zargin 'yan majalisar kasar da kokarin bata masa suna yana mai sanar da 'yan majalisar cewar ba zai bayyana a gabansu kamar yadda suka bukata ba.
-
Akalla Mutane 21 Sun Mutu Sakamakon Fashewar Wata Madatsar Ruwa A Kasar Kenya
May 10, 2018 06:09Rahotanni daga Kenya sun bayyana cewar alal akalla mutane 21 sun rasa rayukansu sakamakon fashewar wata madatsar ruwa saboda ruwan sama da kamar da bakin kwarya da aka yi a daren jiya Laraba wayewar garin Alhamis.
-
Harin Ta'addanci Ya Hallaka Mutane 11 A Somaliya
May 10, 2018 01:54Jami'an 'yan sandar Somaliya sun sanar da mutuwa da kuma jikkatar mutane 21 sanadiyar tashin wani Bam a wata kasuwa dake cikin kasar
-
Tattalin Arzikin Kasashen Kudu Da Sahara Zai Karu A Bana
May 09, 2018 11:58Bankin duniya ya yi hasashen cewa tattalin arzikin kasashen kudu da hamadar sahara zai bunkasu a wannan shekara ta 2018 da muke ciki.
-
Cutar Ebola Ta Sake Bullowa A Congo Kinshasa
May 09, 2018 10:34Hukumomin kiwon lafiya a kasar Congo Kinshasa sun tabbatar da sake barkewar annobar cutar Ebola a kasar, inda ake tsammanin mutane 21 sun harbu da ita, yayin da aka tabbatar da mutane 2 daga cikinsu sun kamu.
-
An Koma Shari'ar Wadanda Ake Zargi Da Juyin Mulki A Burkina Faso
May 09, 2018 10:12A Burkina Faso an koma shari'ar wandanda ake zargi da yunkurin juyin mulki a watan Satumba na shekara 2015 bayan dage zaman sau da dama.