Cutar Ebola Ta Sake Bullowa A Congo Kinshasa
Hukumomin kiwon lafiya a kasar Congo Kinshasa sun tabbatar da sake barkewar annobar cutar Ebola a kasar, inda ake tsammanin mutane 21 sun harbu da ita, yayin da aka tabbatar da mutane 2 daga cikinsu sun kamu.
A sanarwar da ministan lafiya na kasar Orly Ilunga ya fitar a jiya ya ce ana tsammanin mutane 21 dake jihar Equatorial na arewa maso yammacin kasar sun kamu da cutar, inda 17 daga cikinsu suka rasa rayukansu.
Bayanai daga kasar sun ce bisa taimakon hukumar kiwon lafiya ta duniya WHO da kungiyar likitoci ta Doctors Without Borders, an tattara sakamakon bincike 5, inda aka tabbatar da mutane 2 daga cikinsu sun kamu da cutar.
Orly Ilunga ya ce, gwamnatin kasar ta riga ta tura masana da kayayyaki da nufin dakila yaduwar cutar.
A wata sanarwa data fitar, hukumar lafiya ta duniya WHO ta ce ta tura masana don ba da taimako ga gwamnatin kasar, wajen dakile yaduwar cutar mai saurin yaduwa.