Tattalin Arzikin Kasashen Kudu Da Sahara Zai Karu A Bana
https://parstoday.ir/ha/news/africa-i30678-tattalin_arzikin_kasashen_kudu_da_sahara_zai_karu_a_bana
Bankin duniya ya yi hasashen cewa tattalin arzikin kasashen kudu da hamadar sahara zai bunkasu a wannan shekara ta 2018 da muke ciki.
(last modified 2018-08-22T07:01:48+00:00 )
May 09, 2018 11:58 UTC
  • Tattalin Arzikin Kasashen Kudu Da Sahara Zai Karu A Bana

Bankin duniya ya yi hasashen cewa tattalin arzikin kasashen kudu da hamadar sahara zai bunkasu a wannan shekara ta 2018 da muke ciki.

A  rahoton da bankin na duniya ya fitar a baya-bayan nan game da tattalin arzikin kasashen Afirka, ya yi hasashe cewa, a bana karuwar tattalin arzikin kasashen dake kudu da hamadar Sahara zai kai kaso 3.1 bisa dari, kana zai kai kaso 3.6 bisa dari tsakanin shekarar 2019 da 2020.

An yi hasashen ne bisa dogaro da farashin man fetur da iskar gas da kwal da ma'adinai a kasuwar duniya, da kuma matakan gyaran fuskar da wasu kasashen Afirka suka dauka domin kyautata tsarin tattalin arzikinsu.

Saidai masana tattalin arziki irinsu babban masanin tattalin arzikin Afirka na bankin duniya, Albert Zeufack, ya yi nuni da cewa, duk da cewa tattalin azikin kasashen dake kudu da hamadar Sahara zai karu, za a samu ci gaban ne a hankali, ba cikin sauri ba, a don haka dole ne kasashen su kara karfafa gyaran fuskar tsarin tattalin arzikinsu bisa manyan tsare-tsare, ta yadda za su cimma burin samun dauwamamman ci gaba cikin sauri.