DRC : Adadin Mutanen Da Suka Kamu Da Cutar Ebola Ya Kai 11
https://parstoday.ir/ha/news/africa-i30720-drc_adadin_mutanen_da_suka_kamu_da_cutar_ebola_ya_kai_11
Hukumomin kiwan lafiya a Jamhuriya Demokuradiyyar Kango sun ce adadin mutanen da aka tabbatar sun kamu da cutar Ebola a kasar ya karu zuwa goma sha daya.
(last modified 2019-04-27T09:55:10+00:00 )
May 11, 2018 01:23 UTC
  • DRC : Adadin Mutanen Da Suka Kamu Da Cutar Ebola Ya Kai 11

Hukumomin kiwan lafiya a Jamhuriya Demokuradiyyar Kango sun ce adadin mutanen da aka tabbatar sun kamu da cutar Ebola a kasar ya karu zuwa goma sha daya.

Ministan kiwon lafiya na Jamhuriyar Demokuradiyyar Kango, Orly Ilunga ya sanar a daren jiya Alhamis cewa, kawo yanzu, adadin yawan mutanen da aka tabbatar sun kamu da cutar Ebola a yankin Equatorial dake arewa maso yammacin kasar ya kai 11.

Haka kuma akwai wasu ma'aikatan jinya wadanda suka kamu da cutar sakamakon barkewar Ebola a wannan karo, lamarin da ya janyo matukar damuwa a kasar.

Orly Ilunga ya bayyana a wajen taron manema labarai cewa, baya ga cutar Ebola, akwai barkewar sauran wasu masassara a kasarsa.

Game da mutanen da suka rasa rayukansu a kwanan baya, wadanda ake zargin su sun kamu da cutar Ebola kuwa, ministan ya ce, ba za'a iya tabbatar da musabbabin mutuwarsu ba, sai dai bayan an yi gwajin jinin su.