-
Rundunar 'Yan Sandan Nijeriya Ta Sanar Da Fara Shirin Daukar Sabbin 'Yan Sanda 6000
May 03, 2018 12:54A kokarin da ake yi na maganin matsalar tsaro da ake fuskanta a Nijeriya, rundunar 'yan sandan kasar ta sanar da cewa a ranar Litinin mai zuwa (7 ga watan Mayu) za ta fara aiwatar da shirin daukar sabbin 'yan sanda su 6000 kamar yadda shugaban kasar Muhammadu Buhari ya ba da umurni.
-
Sudan Ta Sanar Da Rufe Wasu Ofisoshin Jakadancinta 13 A Kasashen Duniya
May 03, 2018 12:54Shugaban kasar Sudan, Omar Hasan al-Bashir ya ba da umurnin rufe wasu ofisoshin jakadancin kasar su 13 a wasu kasashe daban-daban na duniya a wani mataki na tsuke bakin aljihu da gwamnatin ta shigo da shi sakamakon matsalar tattalin arziki da kasar take fuskanta.
-
Rikici Ya Hallaka Mutum 24 A Kasar Afirka Ta Tsakiya
May 03, 2018 07:22Majiyar asibiti a kasar Afirka ta tsakiya ta sanar da mutuwar mutum 24 sanadiyar rikicin Bangui babban birnin kasar.
-
Wasu 'Yan Ta'adda Sun Kashe Abzinawa 16 A Mali
May 03, 2018 07:19Wasu da ake zargin ‘yan ta’adda ne sun hallaka Abzinawa 16 a arewacin kasar Mali, kwanaki kadan bayan kashe mutane 40 da akayi a wasu kauyukan kasar dake kusa da kan iyaka da kasar Nijer.
-
Shirin Gwamnatin Kaduna A Tarayyar Najeriya Na gabatar Da Sheikh Zakzaky A Gaban Kotu.
May 03, 2018 01:56Shirin Gwamnatin Kaduna a Tarayyar Najeriya Na gabatar Da Sheikh Zakzaky A Gaban Kotu.
-
Nijar : Masarautar Maradi Ta Hana Bidi'o'i A yayin Bikin Aure
May 03, 2018 01:05Masarautar Katsinan Maradi ta jamhuriyar Nijar ta bi sahun takwarorinta na Azbin da Damagaram wajen hana Bidi'o'i a yayin bikin aure.
-
'Yan Bindiga Sun Yi Garkuwa Da 'Yar Agaji A Somaliya_Red Cross
May 03, 2018 01:05Kungiyar agaji ta kasa da kasa ta Red-Cross, ta sanar da cewa wasu 'yan bindiga sun yi garkuwa da wata jami'ar kiwan lafiya a wani gida dake Mogadisho babban birnin kasar Somaliya.
-
IS Ta Dauki Alhakin Kai Harin Ofishin Hukumar Zabe A Libiya
May 03, 2018 00:53Kungiyar 'yan ta'adda ta (IS) ta dauki alhakin kai harin kunan bakin wake da ta ce ya yi sanadin mutuwar mutum a kalla 15 a babban ofishin hukumar zabe na Tripoli.
-
Najeriya : Adadin Mutanen Da Suka Mutu A Hare-haren Mubi Ya Kai 86
May 03, 2018 00:52Rahotanni dake cin karo da juna a Najeriya na cewa, adadin mutanen da suka rasa rayukansu a jerin hare haren Mubi ya kai 86.
-
Har Yanzu Akwai Fargabar Yiwuwar kai Harin Ta'addanci A Arewacin Burkina Faso
May 02, 2018 13:15Ma'aikata a bangaren shari'a a garin Djibo da ke cikin lardin Soum a arewacin kasar Burkina Faso, sun kaurace ma wuraren ayyukansu saboda fargabar yiwuwar kai hare-haren ta'addanci a garin.