May 03, 2018 17:24 UTC
  • Sudan Ta Sanar Da Rufe Wasu Ofisoshin Jakadancinta 13 A Kasashen Duniya

Shugaban kasar Sudan, Omar Hasan al-Bashir ya ba da umurnin rufe wasu ofisoshin jakadancin kasar su 13 a wasu kasashe daban-daban na duniya a wani mataki na tsuke bakin aljihu da gwamnatin ta shigo da shi sakamakon matsalar tattalin arziki da kasar take fuskanta.

Kamfanin dillancin labaran kasar Sudan din (SUNA) ya ce a yammacin jiya Laraba ne shugaba Al-Bashir din ya ba da wannan umurnin ba rufe ofisoshin jakadancin su 13, sannan wasu ofisoshin jakadancin kuma da aka bar su za a rage ma'aikatan wajen zuwa mutum guda, kamar yadda kuma umurni ya sanar da rage kashi 20 cikin dari na ma'aikatun dukkanin ofisoshin jakadancin na Sudan a waje.

Har ila yau kuma sanarwar ta kara da cewa za a rage wani adadi na ma'aikatan Ma'aikatar harkokin waje na kasar ma, kamar yadda ta ce an dau wannan matsaya ne sakamakon irin matsalar tattalin arzikin da kasar ta Sudan take fuskanta.

A kwanakin baya ne dai shugaba Al-Bashir din ya kori ministan harkokin wajen kasara wani abin da ake ganin yana da alaka da korafin da yayi na rashin biyan jami'an diplomasiyyar kasar albashinsu na watanni.

 

Tags