Rikici Ya Hallaka Mutum 24 A Kasar Afirka Ta Tsakiya
Majiyar asibiti a kasar Afirka ta tsakiya ta sanar da mutuwar mutum 24 sanadiyar rikicin Bangui babban birnin kasar.
Kamfanin dillancin labaran kasar Faransa ya nakalto majiyar asibitin kasar Afirka ta tsakiya a wannan alhamis na cewa, rikicin baya-bayan na kwanaki uku da ya auku a birnin Bangui ya yi sanadiyar hallaka mutum 24.
Balkisa Ide Seidou daya daga cikin jami'an kungiyar kare hakin bil-adama na kasa da kasa a kasar ta bayyana cewa matukar dai ba a kame wadanda suka yi sanadiyar wannan tashin hankali ba, to shakka babu rikicin na iya sake barkewa a nan gaba.sannan ta nemi a gurfanar da su a gaban kotu.
Tun a shekarar 2013 ne jamhoriyar Afirka ta tsakiya ta fada cikin rikici sanadiyar rikicin kabilanci da addini.