Pars Today
Mahukunta a Jamhuriyar Afrika ta Tsakiya sun sanar da cewa: An kafa wata kotu ta musamman da zata gudanar da shari'a kan tsoffin shugabannin kasar guda biyu dangane da zargin hannu a kunna wutan yakin basasa a kasar.
Wasu 'yan bindiga sun sace 'yan gudun hijira 9 tare da aiwatar da kisan gilla kansu a garin Bria da ke Jamhuriyar Afrika ta Tsakiya.
Kwamitin tsaron Majalisar Dinkin Duniya ya bukaci kawo karshen tashe-tashen hankula a Jamhuriyar Afrika ta Tsakiya.
Rahotanni daga kasar Afirka ta tsakiya sun bayyana cewar wani sabon rikici mai tsanani ya barke tsakanin kungiyoyi masu dauke da makami da ba sa ga maciji da junansu a kasar.
Dakarun wanzar da zaman lafiya na Majalisar Dinkin Duniya a kasar Afirka ta tsakiya sun yi watsi da zargin da kungiyar Saleka ta yi musu na kisar fararen hula a tsakiyar kasar.
Majiyar asibiti a kasar Afirka ta tsakiya ta sanar da mutuwar mutum 24 sanadiyar rikicin Bangui babban birnin kasar.
Fada tsakanin jami'an tsaro da yan bindiga a birnin Bangi babban birnin Afrika ta tsakiya ya yi sanadiyyar kissan mutane akalla 6.
Kamfanin dillancin labarun Reuters ya ambato majiyar tsaro daga kasar ta Afirka Ta Tsakiya na cewa an kai hari ne da bindigogi da kuma jefa makaman gurneti akan maja'miar.
Majiyoyin dakarun majalisar dinkin duniya masu gudanar da ayyukan wanzar da sulhu da zaman lafiya a jamhuriyar Afirka ta tsakiya sun tabbatar da kai hari a kansu.
Kamfanin dillancin labarun Faransa ya ambato majiyar tsaro daga birnin Bungui na cewa an yi harbe-harbe a kusa da fadar shugaban kasa da ke unguwar PK5.