Sabon Rikici Mai Tsanani Ya Barke A Kasar Jamhuriyar Afirka Ta Tsakiya
Rahotanni daga kasar Afirka ta tsakiya sun bayyana cewar wani sabon rikici mai tsanani ya barke tsakanin kungiyoyi masu dauke da makami da ba sa ga maciji da junansu a kasar.
Kamfanin dillancin labaran kasar Faransa ya jiyo wasu majiyoyin a kasar Afirka ta tsakiyan suna cewa sabon rikicin wanda ya faro daga ranar Larabar da ta gabata ya barke ne tsakanin 'yan tawayen kungiyar Salika da kuma na Anti Balaka a garin Bria da ke tsakiyar kasar.
Duk da cewa har ya zuwa yanzu ba a tantance adadin mutanen da suka mutu ko suka sami raunuka ba, to sai dai wasu majiyoyin sun ce wani adadi mai yawa na masu dauke da makamin da kuma fararen hula ne ko dai suka mutu ko kuma suka sami raunuka sakamakon barkewar rikicin.
Tun daga shekara ta 2013 ne dai kasar Afirka ta Tsakiyan ta fada cikin yakin basasa da yayi sanadiyyar mutuwa da raunana dubun dubatan mutanen kasar.