-
Buhari Ya Gana Da Trump Da Kuma Tattaunawa Kan Batutuwa Daban-Daban Ciki Har Da Batun Ta'addanci
May 01, 2018 00:56Shugaba Muhammadu Buhari na Nijeriya ya gana da kuma tattaunawa da shugaban Amurka Donald Trump kan batutuwa daban-daban musamman kan batun fada da ta'addanci inda shugaban Amurka ya yaba wa shugaba Buharin kan nasarorin da gwamnatinsa take samu a fada da ta'addancin da take yi.
-
Majalisar Kasar Chadi Ta Amince Da Sabon Kundin Tsarin Mulkin Kasar
May 01, 2018 00:56Majalisar dokokin kasar Chadi ta amince da sabon kundin tsarin mulkin kasar da aka yiwa kwaskwarima wanda zai ba wa shugaban kasar Idris Derby daman ci gaba da mulki har zuwa shekara ta 2033 a kan karagar mulki, lamarin da 'yan adawan kasar suka yi watsi da shi.
-
Kotu Ta Bukaci Firayi Ministan Gabon Ya Sauka Kuma A Rusa Majalisa
May 01, 2018 00:55Kotun tsarin mulki ta kasar Gabon ta ba da umurnin firayi ministan da yayi murabus daga mukaminsa sannan kuma a rusa karamar majalisar kasar bayan da aka jinkirta zaban 'yan majalisar da ya kamata a gabatar a makon da ya wuce.
-
An Kai Hari Kan Jami'an Tsaron Nijer A Jahar Difa
Apr 30, 2018 14:46Wata majiyar yankin Difa ta sanar da cewa wasu mahara da ake zaton 'yan boko haram ne sun kai hari kan wani sansanin jami'an tsaro a kusa da kan iyakar kasar da Najeriya
-
An Bukaci Gwamnatin Sudan Ta Janye Sojojinta Daga Kasar Yemen.
Apr 30, 2018 14:42'Yan Majalisar Kasar Sudan sun bukaci janye sojojin kasar cikin gaggawa daga kasar Yemen.
-
Ambaliyar Ruwa Da Zaizayar Kasa Ya Yi Sanadiyar Mutuwar Mutane Da Dama A Kenya
Apr 30, 2018 14:38Kungiyar Agaji ta kasar Kenya ta sanar da mutuwar sama da mutane 100 sanadiyar ambaliyar ruwa da zaizayar kasa da ya auku ciki makunin baya-bayan nan.
-
Kungiyar Yan'uwa Musulmi Na Kasar Masar A Shirye Take Ta Shiga Tattaunawa Da Gwamnati
Apr 30, 2018 08:34Mataimakin shugaban kungiyar Yan'uwa musulmi ta kasar Masar wanda ya bukaci tattaunawa da gwamnatin kasar tare da wasu sharudda guda ukku.
-
An Gudanar Da Zanga-Zangar Yan Allah Wadai Da Safarar Mata Zuwa Saudia Don Aikace-Aikacin Gida
Apr 30, 2018 08:31Wasu kungiyoyin kara hakkin bil'adama a birnin Nuwakhshut na kasar Mauritani sun gudanar da zanga-zangar yin Allah wadai da safarar mata zuwa kasar saudia don aikace aikacen cikin gida.
-
Gwamnatin Kasar Masar Ta Bayyana Cewa Babu Wata hanyar Warware Rikicin Kasar Yemen Sai Ta Tattaunawa
Apr 30, 2018 08:30Ma'aikatar harkokin wajen kasar Masar ta bayyana cewa yakin da ake ta fafatawa a kasar Yeman ba zai kare ba sai ta hanyar siyasa da kuma fahintar juna.
-
Gwamnatin Tarayyar Nigeria Ta Kaddamar Da Wani Shiri Kula Da Cututtuka Wanda Zai Lashe Dalar Amurka Miliyon 90
Apr 30, 2018 08:27Gwamnatin tarayyar Nigeria ta kaddamar da wani shiri na kula da yaduwar cutattuka a kasar wanda zai lakume dalar Amurka miyoyin 90