Kotu Ta Bukaci Firayi Ministan Gabon Ya Sauka Kuma A Rusa Majalisa
Kotun tsarin mulki ta kasar Gabon ta ba da umurnin firayi ministan da yayi murabus daga mukaminsa sannan kuma a rusa karamar majalisar kasar bayan da aka jinkirta zaban 'yan majalisar da ya kamata a gabatar a makon da ya wuce.
Kamfanin dillancin labaran Reuters ya bayyana cewar a jiya Litinin ne dai kotun tsarin mulki ta kasar Gabanon din ta fitar da wannan hukunci inda ta ce sakamakon jinkirta zaben da aka yi don haka firayi ministan kasar Emmanuel Issoze-Ngondet da kuma majalisar dokokin kasar ba su da halalci don haka wajibi ne firayi ministan ya sauka tana mai kiran shugaban kasar Ali Bongo da ya nada firayi ministan rikon kwarya har zuwa lokacin da za a gudanar da zabe.
Firayi minista Emmanuel Issoze-Ngondet din dai, cikin wani jawabi da yayi ta gidan talabijin din kasar ya amince da hukuncin kotun yana mai cewa wajibi ne a aiwatar da shi, kiamar yadda shi ma shugaban majalisar Richard August Onouviet, ya sanar da amincewarsa da hukuncin.
A shekara ta 2016 ne dai shugaba Ali Bongo ya nada Emmanuel Issoze-Ngondet a matsayin firayi ministan kasar bayan lashe zaben shugabancin kasar da yayi a zaben da masu sanya ido na kasa da kasa suka ce an tafka magudi.